Babbar sallah: Buhari shilla garin Daura a yau Juma'a

Babbar sallah: Buhari shilla garin Daura a yau Juma'a

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar babban birnin tarayya Abuja domin zuwa garin Daura da ke Katsina.

Shugaban kasar zai yi hutun Eid-el-Kabi wato babbar sallah a garin na Daura.

Ana sa ran za ayi bikin babban sallar ne a ranar Lahadi.

A yayin da ya ke Daura, shugaban kasar zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar Katsina ta kammala.

DUBA WANNAN: Matakan da zan dauka kan rikicin Majalisun Bauchi da Edo - Buhari

Majiya daga fadar shugaban kasa ta shaidawa The Punch cewa shugaban kasar da ya bar Abuja bayan sallar Juma'a zai dawo Abuja ranar 18 ga watan Augusta.

Buhari zai dawo kwana guda kafin kafa bikin kaddamar da ministoci da za ayi a birnin tarayyar.

Ana sa ran shugaban kasar ne zai bude taron.

Za a kwashe kwanaki biyu ne wurin taron da ake sa ran kammalawa ranar 20 ga watan Augusta sannan a kaddamar da ministoci a ranar 21 ga watan Augusta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel