Boye tikiti: Fasinjoji sun ture jami'an tsaro sun shiga jirgi a tashan jirgin kasa na Abuja

Boye tikiti: Fasinjoji sun ture jami'an tsaro sun shiga jirgi a tashan jirgin kasa na Abuja

Jami'an tsaro da ke tashan jirgin kasa Idu da ke Abuja sun fuskanci fushin fasinjoji a babban birnin tarayya Abuja.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a kwanaki biyu kafin bikin babban sallah.

Channels TV ta ruwaito cewa fasinjojin sun kutsa cikin jirgin da zai tafi Kadfuna da karfin tuwa ba tare da jami'an tsaron sun tantance su ba.

Wasu fasinjojin sun ce sun isa tashan ta wuri ta yadda za su iya sayan tikiti amma a cewarsa wasu ma'aikata a tashan jirgin suna sayar wa wasu shafafu da mai tikitin ko da ba su zo a kan lokaci ba.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Gwamna Matawalle ya nada sabbin sakatarorin kananan hukumomi 14 a Zamfara

A cewar daya daga cikinsu, wasu fasinjoji sun iso tashan tun karfe 11 na safe domin sayan tikitin jirgin da zai tashi karfe 2.20 na rana amma aka ce musu wai tikitin ya kare.

Wani ma'aikacin tashan jirgin da aka nemi ji ta bakinsa ya ce ba zai iya magana ba saboda aiki ya yi musu yawa a halin yanzu.

Ana kyautata zaton mafi yawancin fasinjojin musulmi ne da za su tafi gida hutun babbar sallar da gwamnatin tarayya ta bayar a ranakun Litin da Talata.

A sanarwar da ta fitar a ranar Talata, gwamnatin tarayya ta taya musulmi murnar sallah tare da kira gare su suyi amfani da damar domin yi wa kasa addu'ar samun zaman lafiya da cigaba.

Ta kuma shawarci mutane su guji aikata duk wani abu da ka iya tayar da zaune tsaye sai dai su hada hannu da gwamnati wurin gina kasa da kawo cigaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel