Hajj 2019: Saudiya ta tanadi motocin karta kwana domin daukan mahajjata marasa lafiya

Hajj 2019: Saudiya ta tanadi motocin karta kwana domin daukan mahajjata marasa lafiya

-Gwamnatin Saudiya tayi tanadi na musamman ga maniyyatan da basu da lafiya

-Gwamnatin ta tanadi motocin karta kwana wadanda zasu rika daukan duk maniyyacin da rashin lafiya ta dakatar daga yin wani abu na aikin hajjin

Gwamnatin kasar Saudiya na iya bakin kokarinta ganin cewa dukkanin maniyyata dake kasar kowa ya samu yin aikin hajjinsa lami lafiya. Wannan dalilin ne ya sanya gwamnatin ta tanadi motocin karta kwana domin daukan marasa lafiya daga cikinsu.

Akwai daga cikin mahajjatan da suka iso birnin Madina amma ba su iya kai kan su Makkah saboda halin rashin lafiya. Ma’aikatar lafiyan kasar Saudiya ce ta samar da motocin yin jigilarsu daga Madina zuwa Makkah.

KU KARANTA:Birane 5 mafi kyawon ziyara a duniya

Motocin na karta kwana za su cigaba da zagayawa a wurin tsayuwar Arafa, Mina da kuma masallaci mai tsarki na Makkah domin bada agaji ga marasa lafiya.

A wani labarin kuwa, mun samu kawo maku birane 5 mafiya kyawon ziyara a duniyar nan. Kamar yadda masu iya magana ke fadi, “ Tafiya mabudin ilimi” wannan maganar tasu haka take, saboda mutumin da ke tafiye-tafiye bai taba zama daya wanda kullum yana zaune waje guda.

Wannan manya-manyan biranen guda biyar kuwa su ne: Paris, Rome, Dubai, New York da birnin London. Zan so wata ran mai karatu ziyarci wadannan biranen ko kuma daya daga cikinsu domin ganin yadda suke. Na tabbatar duk wanda ka ziyarta a cikinsu sai ka so ka sake komawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel