Hajjin bana: An sanar da ranar da maniyattan Najeriya za su fara dawowa gida

Hajjin bana: An sanar da ranar da maniyattan Najeriya za su fara dawowa gida

Shugaban sashin jigilar jiragen sama na Hukumar Kula da Maniyyatan Najeriya, NAHCON, Injiniya Mohammed Goni ya ce maniyyatan Najeriya za su fara dawo wa gida Najeriya daga ranar Asabar 17, ga watan Augusta bayan kammala aikin hajji a Saudiyya.

Goni ya bayyana hakan ne wurin wani takaitaccen taro da aka gudanar da masu ruwa da tsaki gabanin Arafat a daren ranar Alhamis.

Ya ce jirgin farko, Flynas Airline zai baro kasa mai tsarki a ranar 17 ga watan Augusta zai dawo da maniyattan Najeriya zuwa Legas.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Gwamna Matawalle ya nada sabbin sakatarorin kananan hukumomi 14 a Zamfara

Ya kara da cewa bisa tarin jigilar maniyattan da Flynas Airline ta bayar, jirage hudu na farko za su dauko maniyyatan Legas ne sannan na biyar zai kwaso maniyattan jihar Kebbi.

Ya shawarci maniyattan su takaita dauko jakunkunan hannu saboda kiyaye dokokin kamfanonin jigilar na kayyade adadin kayan da jirgi zai iya dauka.

"Lokacin da ake bata wa wurin tantance jakunkunan hannun maniyatta ya kan shafi lokacin da jirgi ya kamata ya tashi.

"Idan kuma aka jinkirta tashin jirgi guda daya, hakan zai shafi sauran jiragen," a cewar Mr Goni.

Ana sa ran kamfanonin jiragen sama biyu da za suyi jigilar maniyyatan za su kasance cikin shiri a filin tashi da saukan jirage na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah a ranar 16 ga watan Augusta domin fara shirin dawo da maniyattan Najeriya gida.

Kamfanonin jiragen sune MaxAir da Flynas saboda na ukunsu Medview bai samu ikon jigilar ba saboda karancin jirage.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel