Uwargidar gwamna ta fara horas da yan mata fadar Taekwando don yaki da fyade

Uwargidar gwamna ta fara horas da yan mata fadar Taekwando don yaki da fyade

Uwargidar gwamnan jahar Ondo, Betty Akeredolu ta dauki hayan wasu kwararru a fagen dabarun fara irin na Taekwando, wanda aka fi sani da Chanis, domin su horas da yan mata yadda zasu kare kansu daga masu fyade.

Uwargida Betty ta bayyana haka ne a ranar Juma’a, 9 ga watan Yuli yayin da take ganawa da kwamishinan Yansandan jahar Ondo, Undie Adie, inda ta bayyana damuwarta game da karuwar fyade fyade a jahar.

KU KARANTA: Dama ta samu: Hukumar tsaro ta farin kaya tana daukan aiki a yanzu

Matar gwamnan ta kai ziyara ga kwamishina ne bisa rahoton daya watsu na yi ma wata dalibar jami’ar Adekunle Ajasin fyade da wasu jami’an rundunar Sojan Najeriya suka yi mata a daidai shingen binciken ababen hawa.

Betty ta bayyana aniyarta na tashi tsaye a kan matsalar fyade, sa’annan ta nemi Yansanda su tabbata an hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan laifi ta hanyar gurfanar dasu a gaban kotu.

A cewarta, kamata ya yi ace Sojoji suna kare lafiyar yan Najeriya, amma sai gashi ana zaton wuta a mekera an tsinceta a masaka, don haka tace wannan ya nuna matan Ondo suna cikin hadari kenan, da wannan dalili tasa dole ne ta fara koya musu fadan Taekwando don kare kansu.

Da yake jawabi, kwamishinan Yansandan jahar, Undie Adie ya bata tabbacin ganin an hukunta duk wadanda suka aikata fyade a kan daliban, yace da zarar hukumar Soji ta mika mata Sojoji, za ta dauki matakin daya dace a kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel