Kwamitin bincike sun saki hotunan wajen da aka kashe jami’an yan sanda

Kwamitin bincike sun saki hotunan wajen da aka kashe jami’an yan sanda

Wani kwamiti da hukumar yan sanda ta kafa domin binciken kisan jami’anta uku da wani dan farin hula a ranar Juma’a, 9 ga watan Agusta sun ziyarci wajen da lamarin ya afku.

Lamarin ya afku ne a ranar Laraba, 7 ga watan Agusta a hanyar Ibi-Wukari, jihar Taraba lokacin da jami’an ke aikin bincike a yanki.

A cewar kakakin rundunar, DCP Frank Mba, jami’an sun je kama wani Alhaji Hamisu ne wanda ke da hannu garkuwa da mutane.

Amma da suke martani kan lamarin, hukumar soji ta yi ikirarin cewa an samu kuskure ne kan lamarin, yayinda dakarun bataliya 93 Takum, suka kuskuren daukarsu a matsayin masu garkuwa da mutane sannan suka yi musayar wuta da su.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: EFCC ta sake kama surukin Atiku da lauyansa

Kalli hotunan kwanitin binciken karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan yan sanda, Abba Kyari a wajen da lamarin ya afku a kasa:

Kwamitin bincike sun saki hotunan wajen da aka kashe jami’an yan sanda

Kwamitin bincike sun saki hotunan wajen da aka kashe jami’an yan sanda
Source: UGC

Kwamitin bincike sun saki hotunan wajen da aka kashe jami’an yan sanda

Kwamitin bincike sun saki hotunan wajen da aka kashe jami’an yan sanda
Source: UGC

A wani labarin kuma, mun ji cewa kashe wani direba da jami'an tsaro su kayi a hanyar Kaduna zuwa Abuja ya janyo direbobin sun fara zanga-zanga wacce ta janyo cinkoso a hanyar.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron sun harbe direban Peugeot J-5 din ne a kusa da Olam misalin karfe 7.30 na safe a hanyarsa ta zuwa Kaduna.

Sauran direbobin sun ga abinda ya faru hakan ya sa suka ajiye motocin su a kan titi suna zanga-zangar rashin amince wa da irin wannan kisar gillar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel