Za a fara jigilar dawo da alhazan Najeriya a ranar 17 ga watan Agusta

Za a fara jigilar dawo da alhazan Najeriya a ranar 17 ga watan Agusta

Rahotanni sun kawo cewa za a fara jigilar dawo da lhazan Najeriya daga ranar Asabar, 17 ga watan Agusta, 2019 bayan kammala aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya.

Shugaban kula da harkokin jirgin sama a hukumar da ke kula da mahajjatan Najeriya (NAHCON), Injiniya Mohammed Goni, ne yayi dan takaitaccen bayani aka dawowar a wani taron kafin ranar Afara tare da masu ruwa da tsaki a Makkah a daren ranar Alhamis, 8 ga watan Agusta.

Injiniya Goni, wanda yace jirgin farko daga kamfanin Flynas, da ke dauke da alhazan jihar Lagas zai tashi da karfe 7:00 na ranar 1 ga watan Agusta., inda ya kara da cewa bisa ga shirin Flynas, jirage hudu na farko zai kwashi alhazan Lagas yayinda na biyar zai kwashi na jihar Kebbi.

Ya bukaci jami’ai daga hukumar aikin hajji na jihar da su hada kai da hukumar sannan su tabbatar da cewa mahajattan ba su dauki jakunkuna da yawa ba a hannu.

KU KARANTA KUMA: Mahajjatan Najeriya 6 sun rasu a kasar Saudiyya

Ana sanya ran cewa jirage biyu da za su kwashi mahajjata za su kasance a filin jirgin sama na sarki Abdlaziz, Jeddah, a ranar 16 ga watan Agusta, domin fara dawowa Najeriya.

Jiragen sune MaxAir da Flynas, yayinda na uku Medview, ba zai samu damar aiki ba saboda rashin jirgi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel