Yanzu Yanzu: EFCC ta sake kama surukin Atiku da lauyansa

Yanzu Yanzu: EFCC ta sake kama surukin Atiku da lauyansa

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), ta sake kama mutane biyu kuma makusanyan dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Dmocratic Party (PDP).

An tsare Uyi Giwa Osagie, mai ba Mista Atiku shawara akan lamarin doka, da kuma Abdullahi Babalele, surukin tsohon mataimakin Shugaban kasar a yammacin ranar Alhamis, 8 ga watan Agusta, jaridar Premium Times ta ruwaito.

An kama su ne bayan amsa gayyatar hukumar EFCC a jihar Lagas, cewar wasu majiyoyi.

Wani kakakin hukumar EFCC, Tony Orilade, ya fada ma majiyarmu cewa yana bukatar Karin lokaci domin yin sharhi akan kamun nasu.

Sai dai kuma an tattaro cewa hukumar na shirin gurfanar da Mista Giwa-Osagie kan zargin zambar wasu kudade.

Zuwa yanzu dai hukumar bata tabatar da ko wannan sabon kamun, karashe ne na tsohuwar binciken da suka akansu.

KU KARANTA KUMA: Ana wata ga wata: PDP ta kalubalanci hukumar DSS akan sace Dadiyata

Idan za ku tuna Legit.ng ta rahoto a baya cewa EFCC a ranar Litinin, 4 ga watan Maris tace tana binciken Alhaji Babalele Abdullahi, daraktan kudi na kamfanonin Atiku Abubakar kan zargin satar kudade.

Abdullahi ya kasance suruki ga Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa da aka kayar a karkashin jam' iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel