Ana wata ga wata: PDP ta kalubalanci hukumar DSS akan sace Dadiyata

Ana wata ga wata: PDP ta kalubalanci hukumar DSS akan sace Dadiyata

Jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta kalubalanci hukumar tsaro na sirri (DSS), da ta yi magana kan ikirarin cewa jami’anta na da hannu a sace babban dan kwankwasiyyan nan, Abubakar Idris wanda aka fi sani da Abu Hanifa Dadiyata.

Jam’iyyar tace ba zai yiwu DSS ta ci gaba da yin shiru akan sace Dadiyata wanda aka yi garkuwa dashi tun ranar Juma’a da ya gabata ba.

A wani jawabi da kakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ya saki a ranar Alhamis, 8 ga watan Agusta, ya ce akwai ikirari a shafukan sadarwa da ke cewa jami’an DSS na da hannu a sace Dadiyata, bisa umurnin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

PDP ta bayyana matsayarta ne kan la’akari da cewa an san Dadiyata da sukar manufofin APC da gwamnatinta, musamman a jihar Kano inda a nan ne aka sace shi.

Jawabin yace: “Akwai rade-radin cewa sace Dadiyata da aka yi zuwa wani waje dab a a sani ba baya rasa nasaba da kokarin son razanar dashi da kuma rufe masa baki da kuma kokarin hana mutane fadar ra’ayinsu a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin APC sun ce jam’iyyar ta kara tabarbarewa a karkashin Oshiomhole

“Don haka PDP na bukatar hukumar DSS da tayi Magana sannan ta dauki matakan gaggawa wajen kwato Dadiyata daga wadanda suka yi garkuwa dashi tun kafin lokaci ya kure.

“Musamman saboda yanzu zukata sun dau zafi sannan duk wani jikiri wajen sakin Dadiyata na iya tunzura mutanenmu, musamman a jihar Kano, inda yake da mabiya da yawa.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel