ATBU: Dalibai 30 na akan gada suna daukar hotunan selfie kafin ya rufta – Shugaban makarantar

ATBU: Dalibai 30 na akan gada suna daukar hotunan selfie kafin ya rufta – Shugaban makarantar

Muhammad Abdullazeez, Shugaban jami’ar Abubakar Tafawa Balewa University (ATBU), Bauchi, yace sama da dalibai 30 ne suke daukar hotunan selfie akan gadar masu wucewa kafin ya rufta kwanaki uku da suka gabata.

A ranar Litinin ne wani gada da ke sada dakunan kwana da dakunan karatu ya rufta, sakamakon ambaliyar ruwa da ya faru bayan ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya.

Don haka, hukumar jami’ar ta sanar da rufe ayyukan makarantar na yan kwanaki domin karrama daliban da suka rasa rayukansu a lamarin.

Da yake magana a ranar Laraba, lokacin da ya karbi bakuncin Bala Mohammed, gwamnan jihar, wanda ya kai masa ziyarar jaje zuwa sansanin Gubi na jami’ar, Shugaban makarantar ya daura laifi akan daliban na jijjiga gadar ayinda suke daukar hotunan selfie.

A cewarsa, gadar na da karfin daukar mutane 15 ne kacal a lokaci guda sannan cewa ba a gina shi ta yadda zai dauki lodi da yawa ba. Ya kara da cewa sai gashi daliban sun taru akan gadar domin daukar selfie.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin APC sun ce jam’iyyar ta kara tabarbarewa a karkashin Oshiomhole

Ya kuma yi watsi da ikirarin cewa mutane hudu ne suka mutu sannan kuma cewa da dama sun bata ba a gansu ba har yanzu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel