Gwamnonin APC sun ce jam’iyyar ta kara tabarbarewa a karkashin Oshiomhole

Gwamnonin APC sun ce jam’iyyar ta kara tabarbarewa a karkashin Oshiomhole

Kungiyar gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress, sun caccaki Shugaban jam’iyyar ta APC na kasa, Adams Oshiomhole, akan rikirkita lamarin jam’iyyar.

Darakta-Janar na kungiyar, Salihu Lukman, a wata wasika mai taken: “APC: Rokon yin sulhu, mai kwanan wata 6 ga watan Agusta, 2019, zuwa tsohon Shugaban kungiyar kwadagon, yace abubuwa sun kara tabarbarewa a jam’iyya mai mulki.

Lukman ya lura cewa babu wani banbanci a tsakanin yadda Oshiomhole ke tafiyar da jam’iyyar da kuma yadda Cif John Odigie-Oyegun ya tafiyar da ita a lokacin shugabancinsa.

“Maimakon haka abubuwa sun kara tabarbarewa da munana. Matsalolin shugabanci da jam’iyyar ke fuskanta na kara zurfafa a halin da ake ciki,” inji shi.

Kungiyar ta alakanta faduwar da suka yi a zaben gwamna a jihohin Zamfara, Oyo, Imo, Bauchi da Adamawa ga rikcin cikin gida da Shugaban na APC ya haddasa, inda tayi gargadin cewa hakan na iya kasancewa a Kogi, Ondo da Edo.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An sake kashe wani dan Najriya a kasar Afrika ta kudu

Ya bukaci tsohon gwamnan na jihar Edo da bayar da damar tattaunawa domin nemo maslaha ga matsalolin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel