Yanzu Yanzu: An sake kashe wani dan Najriya a kasar Afrika ta kudu

Yanzu Yanzu: An sake kashe wani dan Najriya a kasar Afrika ta kudu

Yan bindiga sun sake kasha wani dan Najriya mai tukin tasi, Joseph Ajouna, a kasar Afrika ta Kudu.

Hakan na zuwa ne kasa da mako guda bayan an kasha wani dan Najriya mai suna Benjamin Simeon, wanda shima matukin tasi n da ya fito daga yankin Okposi, jihar Ebonyi, inda aka kashe shi a Johannsburg a ranar 3 ga watan Agusta.

Da yake bayanin lamarin, Shugaban kungiyar yan Najeriya, a yankin Western Cape Province, Mista Charles Eleberi, yace wanda aka kashe ya fito ne daga yankin Umahia Ubeku a jihar Abia, sannan kuma cewa wasu fasinjoji da ya je dauka a Nyanga, Cape Town, da ke Afrika ta Kudu ne suka chakesa sau da dama.

Mista Eleberi ya kuma bayyana cwa an sace mota da kayayyakin Ajouna sannan aka kaddamar da mutuwarsa bayan an isa asibiti.

A watan Yuli, yan sandan Nyanga sun yi kira ga direbobin tasi da su guji yankunan Browns Farm Crossroads da Nyanga domin yan fashi da masu kwace na far ma direbobi.

KU KARANTA KUMA: Babu ruwana da shafuka da ke dangantani da goyon bayan masu yi wa Buhari bore – Namadi Sambo

Sai dai kuma babban kwamishinan Najeriya, Ambassador Kabir Bala, tare da sauran jami’an hukumar sun ziyarci matar marigayin mai ciki da yara biyu, inda suka yi alkawarin cewa za su ta bibiyar shari’ar har sai an kama wadanda suka aikata laifin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel