An shiga uku: Hankula sun tashi yayin da yanayin zafi ya kashe mutane 2,964

An shiga uku: Hankula sun tashi yayin da yanayin zafi ya kashe mutane 2,964

Akalla mutane 2,964 ne suka mutu sakamakon zazzafan yanayi da ake fama da shi a kasar Netherland, yanayin da a yanzu haka ya mamaye kafatanin nahiyar Turai gaba daya, inji rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito adadin mutanen da suka mutu a bana ya haura adadin mutanen da suka mutu a bara da kusan mutuwa 400. Wannan yanayi na zafi ya bayyana ne tun daga ranar 22 ga watan Yuli.

KU KARANTA: Zakzaky ba matsoraci bane kamarka, ba zai tsere daga Najeriya ba – Yan Shia ga El-Rufai

Tun a shekarar 2006 rabon da samu irin wannan tsananin zafi a kasar Netherlands, inda a yanzu haka yanayin ya kai digiri 40 a ma’aunin Celcius. Rahotanni sun bayyana cewa tsofaffi yan shekara 80 zuwa sama guda 300 ne suka mutu a wannan hali.

Al’ummar kasar Netherland da basu haura miliyan 17 ba sun tsinci kansu cikin wannan mawuyacin hali ne sakamakon karuwar dumamar yanayi da ake samu saboda yawan fitar da hayaki da kamfanoni suke yi cikin sararin samaniya.

A wani labari kuma, wata Mata yar Najeriya kuma Musulma, Zulfat Suara nag aba da kafa tarihi a kasar Amurka, idan har ta lashe zaben maimaici da za’a gudanar a ranar 12 ga watan Satumba na majalisar dokokin jahar Tennessee.

Idan har Zulfat ta lashe wannan zabe inda za ta wakilci yankin Nashville, za ta zamo Musulma ta farko yar Najeriya da ta fara shiga majalisar dokokin jahar Tennessee.

Nashville ne babban birnin jahar Tennessee, kuma Zulfat za ta fafata ne da dan majalisa mai ci, Bob Mendes, sai dai Zulfat tace mutane da dama basu dauketa da muhimmanci ba a zaben, amma sai ga shi ta basu mamaki bayan zaben farko da aka yi a ranar 1 ga watan Agusta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel