Yau Buhari zai tafi Daura hutun babbar sallah

Yau Buhari zai tafi Daura hutun babbar sallah

-Shugaba Buhari zai tafi Daura hutun babbar sallah a yau Juma'a

-Shugaban kasan zai kasance a jihar Katsina har sai hutun sallah ya kare inda ake sa ran dawowarsa Abuja

-Akwai ayyukan da ake tsammanin Shugaba Buhari zai kaddamar a Katsina kafin ya gama hutun nasa

Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Abuja zuwa Daura dake jihar Katsina domin yin hutun babbar sallah wadda za ta kama a ranar Lahadin dake tafe.

Majiyar Daily Trust ta tattaro mana bayanan cewa, Shugaban kasan zai bar Fadar Villa ne da zarar an kammala sallar Juma’a.

KU KARANTA:APC na tsaka mai wuya: Wasu na hannun daman shugaba Buhari sun sauya sheka tare da sama da mutane 6,000 daga jam'iyyar APC zuwa PDP a jihar Zamfara

A ranar Lahadi ne dukkanin musulmin Najeriya za suyi bikin sallar ta layya kamar yadda sauran musulmin duniya za suyi.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana ranakun Litinin da Talata a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bikin sallah babba, inda za a koma kan aiki a ranar Laraba.

Rabon Shugaban kasa da Daura tun lokacin babban zaben da aka yi cikin shekarar nan, a na sa ran Shugaban kasan zai kaddamar da wasu ayyukan a Katsina kafin hutun nasa ya kare.

Haka zalika, Shugaban kasa zai kasance a Jihar Katsina har sai hutun sallar ya kare kamar yadda rahoton Daily Trust ya fadi.

A wani labarin kuwa, za kuji cewa Shugaban yakin neman zaben shugaba Buhari na shekarar 2019 dinnan a jihar Zamfara, Alhaji Bature Sambo, ya sauya sheka daga jam'iyyar APC mai mulki inda ya koma babbar jam'iyyar adawa ta PDP tare da wasu manya a jam'iyyar na jihar, a ranar Alhamis dinnan 8 ga watan Agusta.

Da yake magana a lokacin da suke sauya shekar a gidan gwamnatin jihar ta Zamfara dake Gusau, Sambo ya bayyana cewa yanayin aikin gwamnan jihar, Bello Matawalle ne yasa ya ji sha'awar dawowa jam'iyyar ta PDP, inda ya ce ba a jima da rantsar dashi ba, amma har ya samo bakin zaren 'yan bindigar da suka addabi jihar shekarun da suka gabata. Inda ya kuma bayyana cewa gwamnan jihar Abdul'aziz Yari ya kasa yin abinda gwamnan nan yanzu yayi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel