APC na tsaka mai wuya: Wasu na hannun daman shugaba Buhari sun sauya sheka tare da sama da mutane 6,000 daga jam'iyyar APC zuwa PDP a jihar Zamfara

APC na tsaka mai wuya: Wasu na hannun daman shugaba Buhari sun sauya sheka tare da sama da mutane 6,000 daga jam'iyyar APC zuwa PDP a jihar Zamfara

- Shugaban yakin neman zaben shugaba Buhari na shekarar 2019 a jihar Zamfara ya canja sheka tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar a jihar zuwa jam'iyyar PDP

- Shugaban yakin Buharin ya bayyana cewa yanayin aikin gwamnan jihar na yanzu Alhaji Bello Matawalle shine yasa yaji yana son komawa jam'iyyar PDP din

- Haka kuma banda jiga-jigan jam'iyyar, akwai sama da mutane dubu shida da suka sauya shekar suka koma jam'iyyar PDP din

Shugaban yakin neman zaben shugaba Buhari na shekarar 2019 dinnan a jihar Zamfara, Alhaji Bature Sambo, ya sauya sheka daga jam'iyyar APC mai mulki inda ya koma babbar jam'iyyar adawa ta PDP tare da wasu manya a jam'iyyar na jihar, a ranar Alhamis dinnan 8 ga watan Agusta.

Da yake magana a lokacin da suke sauya shekar a gidan gwamnatin jihar ta Zamfara dake Gusau, Sambo ya bayyana cewa yanayin aikin gwamnan jihar, Bello Matawalle ne yasa ya ji sha'awar dawowa jam'iyyar ta PDP, inda ya ce ba a jima da rantsar dashi ba, amma har ya samo bakin zarem 'yan bindigar da suka addabi jihar shekarun da suka gabata. Inda ya kuma bayyana cewa gwamnan jihar Abdul'aziz Yari ya kasa yin abinda gwamnan nan yanzu yayi.

KU KARANTA: Allah ya kyauta: Soja ya harbe wani dan acaba har lahira saboda ya hana shi cin hancin naira 100

Sambo ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP tare da shugaban zartarwa na asibitin tarayya dake Port Harcourt jihar, Alhaji Muktari Anka, tsohon kwamishinan matasa na jihar, Alhaji Abdullahi Mohammed, tsohon mai bada shawara na musamman, Alhaji Ibrahim Ajala da kuma sama da mutane dubu shida da suke jam'iyyar APC.

Da yake karbar masu sauya shekara, Gwamnan jihar Bello Matawalle ya bayyana cewa ba zasu nuna banbanci ba tsakaninsu da tsofaffin jam'iyya, sannan kuma ya yayi gargadi da magoya bayan tsohuwar gwamnati da su bi doka a jihar idan ba haka ba zai dauki hukunci mai tsanani a kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel