Allah ya kyauta: Soja ya harbe wani dan acaba har lahira saboda ya hana shi cin hancin naira 100

Allah ya kyauta: Soja ya harbe wani dan acaba har lahira saboda ya hana shi cin hancin naira 100

- Wani jami'in hukumar soji ya harbe wani dan acaba da ya fito neman na abincin har lahira

- Sojan ya harbi mutumin ne saboda ya hana shi cin hancin naira dari (N100) da suke karba a wajen mutane idan suka biyo ta wajen su

- Wannan lamari ya jawo wasu fusatattun matasa yunkurowa inda suka kone wata motar 'yan sanda da suke wajen don kwantar da tarzoma

An samu wani rikici a yankin Opobo na awanni da yawa bayan wani jami'in hukumar soji ya harbe wani dan acaba wanda aka fi sani da Okada har lahira.

A rahoton da muka samu, sojan ya kashe dan acaban ne saboda ya hana shi cin hancin naira dari (N100) a wajen da suke yin binciken ababen hawa.

An bayyana cewa dan acaban bai dade da matarsa ta haihuwa ba yana ta fafutukar yadda zai nema musu kudin abincin da zasu saka a bakunan su wannan lamari ya faru.

KU KARANTA: Tashin hankali: An kama wani saurayi da tsananin karfin sa yasa karuwa ta mutu a lokacin da yake saduwa da ita a otel

Sannan rahotanni sun bayyana cewa wannan lamari ya jawo wasu fusatattun matasa sun kone wata motar 'yan sanda da suke wajen don kwantar da tarzomar.

A cikin wannan makon ne dai muka kawo muku rahoton yadda sojoji suka harbe wasu 'yan sanda guda uku, inda suka bayyana cewa basu san cewa jami'an 'yan sanda bane, lamarin da a yanzu yake jawo kace nace a tsakanin hukumar 'yan sanda da ta soji kenan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel