Hukumar aikin Hajji ta karrama Limamin daya ceci Kiristocin Berom 300, a Saudiya

Hukumar aikin Hajji ta karrama Limamin daya ceci Kiristocin Berom 300, a Saudiya

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta karrama wasu Musulmai yan Najeriya guda biyu da suka nuna kyawawan halaye abin koyi, a yayin aikin Hajji na bana.

Legit.ng ta ruwaito wadannan mutane biyu sun hada ne da Imam Abubakar Abdullahi, limamin wani Masallaci dake jahar Filato wanda ya ceci wasu kiristoci yan kabilar Berom fiye da 300 daga harin yan bindiga, da kuma Kofur Bashir Umar, Sojan daya tsinci N15,000,000 kuma ya mayar.

KU KARANTA: Rundunar Yansanda ta yi ma rundunar Soji tambayoyin kurilla guda 5 game da kisan jami’anta

Hukumar aikin Hajji ta karrama Limamin daya ceci Kiristocin Berom 300, a Saudiya

Imam da Bashir
Source: Facebook

Hukumar NAHCON ta karrama Imam Abubakar ne ta hanyar sanyashi cikin tawagar Malaman Hajji ta kasa da zasu gudanar da wa’azuzzuka da tunatarwa ga mahajjatan Najeriya a yayin aikin Hajji.

Haka zalika hukumar ta karrama Kofur Bashir Umar ta hanyar sanyashi daga cikin jami’an kwamitin tsaro na hukumar da zasu kula da tsaron alhazan Najeriya da dukiyoyinsu a yayin zamansu a kasar Saudiyya.

A wani labarin kuma, wata Mata yar Najeriya kuma Musulma, Zulfat Suara nag aba da kafa tarihi a kasar Amurka, idan har ta lashe zaben maimaici da za’a gudanar a ranar 12 ga watan Satumba na majalisar dokokin jahar Tennessee.

Jaridar Guardian ta ruwaito idan Zulfat ta lashe wannan zabe inda za ta wakilci yankin Nashville, za ta zamo Musulma ta farko yar Najeriya da ta fara shiga majalisar dokokin jahar Tennessee.

Nashville, shi ne babban birnin jahar Tennessee, kuma Zulfat za ta fafata ne da dan majalisa mai ci, Bob Mendes, sai dai Zulfat tace mutane da dama basu dauketa da muhimmanci ba a zaben, amma sai ga shi ta basu mamaki bayan zaben farko da aka yi a ranar 1 ga watan Agusta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel