Zakzaky ba matsoraci bane kamarka, ba zai tsere daga Najeriya ba – Yan Shia ga El-Rufai

Zakzaky ba matsoraci bane kamarka, ba zai tsere daga Najeriya ba – Yan Shia ga El-Rufai

Kungiyar Shia ta IMN ta mayar da martani ga tsauraran sharuddan da gwamnan jahar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya gindaya ma shugabanta, Ibrahim Zakzaky da matarsa Zeenatu, da nufin su yarda dasu kafin a basu daman tafiya kasar Indiya don duba lafiyarsu.

Kungiyar ta bayyana cewa Zakzaky ba zai gudu daga Najeriya kamar yadda El-Rufai ya yi a shekarar 2007, zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua ba, don haka Zakzaky ba matsoraci bane kamarsa.

KU KARANTA: Rundunar Yansanda ta yi ma rundunar Soji tambayoyin kurilla guda 5 game da kisan jami’anta

Shugaban kungiyar Free Zakzaky, Abdulrahman Abubakar ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 8 ga watan Agusta, inda yace Zakzaky dan Najeriya ne, kuma ba gudu daga kasarsa zuwa wata kasa don neman mafaka ba, don haka zai dawo Najeriya da zarar an sallameshi daga Asibiti.

Idan za’a tuna a ranar Litinin, 5 ga watan Agusta ne wata kotun jahar Kaduna ta yanke hukuncin sakin Zakzaky da matarsa domin su duba lafiyarsu a wani Asibiti dake kasar Indiya da sharadin jami’an gwamnati zasu sa musu ido yayin zamansu a asibitin.

Sai dai a ranar Laraba, 7 ga watan Agusta gwamnatin jahar Kaduna ta fitar da wasu sabbin sharudda tsaurara guda 7 da ta bukaci Zakzaky ya amince dasu kafin ta bashi daman tafiya kasar Indiyan, wanda hakan bai yi ma yan Shia dadi ba.

“Yan Najeriya ba zasu manta yadda El-Rufai ya gudu daga Najeriya a shekarar 2007 ba, kuma a yanzu Alkali bada umarnin sakin Zakzaky, sa’annan hukumar DSS ta yi alkawarin cika wannan umarni, don haka bamu ga dalilin da gwamnatin Kaduna za ta kawo wasu sabbin sharudda ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel