Gwamna El-Rufai ya nada shuwagabannin hukumomin gwamnati 15

Gwamna El-Rufai ya nada shuwagabannin hukumomin gwamnati 15

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya amince da nadin wasu mutane 15 domin shugabantar wasu hukumomin gwamnatin jahar Kaduna, kamar yadda sanarwa daga fadar Sir Kashim Ibrahim ta tabbatar.

Legit.ng ta ruwaito sanarwar na dauke da sa hannun babban hadimin gwamnan jahar Kaduna a kan harkokin watsa labaru, Mista Muyiwa Adekeye, inda ta bayyana cewa gwamnan ya kara ma wasu jami’an gwamnati 3 girma da wannan mukami.

KU KARANTA: An yi turereniya wajen kwasan wasu miliyoyin kudi da suka antayo daga cikin Motar banki

1. Dr. Baka Isah, shugaban hukumar yaki da cutar kanjamau

2. Dr. Joseph Maigari, shugaban hukumar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi

3. Ibrahim Ismaila Ahmed, shugaban hukumar gidan rediyon jahar Kaduna

4. Basheer Bature, shugaban hukumar kididdigan alkalumma ta jahar Kaduna

5. Bashir Muhammad, shugaban hukumar sauye sauye a aikin gwamnati

6. Engr. Lawal Magaji, shugaban hukumar kula da titunan jahar Kaduna

7. Aisha Saidu Bala, shugaban hukumar sufuri ta jahar Kaduna

8. Ismail Umaru Dikko, shugaban KASUPDA

9. Dominic Bincike Dogo, shugaban hukumar cigaban unguwanni na jahar Kaduna

10. Dr. Muhammad Nura Sani, shugaban hukumar hakar ma’adanan kasa

11. Umar Waziri, shugaban hukumar zuba hannun jari ta Kaduna

12. Hadiza Hamza, shugaban hukumar kula da kadarorin gwamnati

13. Mohammed Dayyabu Paki, shugaban hukumar kula da kayayyakin gwamnati

14. Kabir Goma, shugaban hukumar farfado da kamfanonin Kaduna

15. Lawal Jibrin, shugaban hukumar kula da muhallin jahar Kaduna

Daga karshe sanarwar ta bayyana cewa nadin ya fara aiki ne nan take ba tare da wata wata ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel