Rundunar Yansanda ta yi ma rundunar Soji tambayoyin kurilla guda 5 game da kisan jami’anta

Rundunar Yansanda ta yi ma rundunar Soji tambayoyin kurilla guda 5 game da kisan jami’anta

Rundunar Yansandan Najeriya ta yi fatali da bayanin da rundunar Sojan kasa ta Najeriya ta yi game da dalilin da yasa Sojoji suka bude ma jami’anta wuta a jahar Taraba har suka kashe mutane 3, tare da jikkata wasu da dama.

Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da Yansanda suka kamo wani kasurgumin barawon mutane, Alhaji Hamisu Bala Wadume, inda a dalilin wannan hari da Sojoji suka kai barawon ya tsere, har yanzu ba’a san inda ya shiga ba.

KU KARANTA: An yi turereniya wajen kwasan wasu miliyoyin kudi da suka antayo daga cikin Motar banki

A jawadin rundunar Sojoji, tace ta samu rahoton cewa wasu masu garkuwa da mutane sun saci Alhaji Hamisu ne, don haka ta tura Sojojinta domin su taresu, kuma duk kokarin da Sojojin suka yin a dakatar da motar mutanen ta ci tura, don haka suka bude musu wuta sakamakon mutanen basu bayyana ko su wanene su ba, a cewarsu basu san Yansanda bane.

Sai dai rundunar Yansandan ta gabatar da wasu kwararan tambayoyin kurilla guda 5 ga rundunar Sojan kasa kamar haka, wadanda tace tana bukatar rundunar Sojan ta baiwa yan Najeriya gamsashshen amsa.

- A yanzu ina kasurgumin barawon mutane, Alhaji Hamisu Bala Wadume ya shiga da Sojoji suka ce sun ceceshi ne?

- Menene dalilin da yasa Sojoji suka saki Alhaji Hamisu Bala Wadume, kuma ta yaya suka sakeshi?

- Ya za’a yi ace mutumin dake daure da ankwa ya tsere daga hannun Sojoji da suka kwaceshi?

- Me yasa Sojoji basu tafi da Alhaji Hamisu Bala Wadume zuwa ofishinsu don amsa tambayoyi idan har da gaske saceshi aka yi ba?

- Me yasa Sojoji suka harbi Yansanda a gab-da-gab duk da cewa bidiyo ya nuna Yansandan sun bayyana ko su wanene so ga Sojojin?

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel