Buhari ya nuna alhini akan mutuwar matar tsohon gwamnan Taraba

Buhari ya nuna alhini akan mutuwar matar tsohon gwamnan Taraba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 8 ga wata Agusta, ya mika ta’aziyyarsa zuwa ga iyalan Alhaji Garba Umar wanda ya kasance tsohon Gwamnan jihar Taraba, akan mutuwar matarsa, Hajiya Hadiza Garba Umar.

A wata wasika da tawagar gwamnatin Tarayya suka gabatar a madadinsa, Shugaban kasa Buhari yace, “ina mai bakin ciki akan labarin mutuwar matarka Hajiya Hadiza. Dan Allah ka mika ta’aziyyana zuwa ga iyalanka gaba daya. Allah yasa ta huta.

"Ina addu'a kan Allah madaukakin sarki ya ji kan marigayiyar da kuma baka juriyar wannan babban rashi tare da iyalanka baki daya" inji shugaban kasar.

Tawagar sun kunshi Sarki Abba da Garba Shehu, manyan hadiman shugaban kasar kan harkokin cikin gida da kuma kafofin yada labarai; likitan Shugaban kasa, Dr. Suhayb Rafindadi; da kuma shugaban tsarin dokokin fadar shugaban kasa, Ambassador Lawal Kazaure.

KU KARANTA KUMA: Tsananin talauci ne ya jefa ni harkar garkuwa da mutane - Mai laifi

Alhaji Umar ya jinjina wa shugaban kasar akan aika tawagar da yayi domin su mika gaisuwar ta’aziyya, ya kuma yi addu’a akan zaman lafiya da cigaban kasa baki daya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel