Yanzu Yanzu: Gwamnan jihar Bauchi ya yiwa Oshiomhole wankin babban bargo

Yanzu Yanzu: Gwamnan jihar Bauchi ya yiwa Oshiomhole wankin babban bargo

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bayyana cewa Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole, na shirin jefa tsarin zaman lafiyar siyasar jihar cikin hatsari.

A wani jawabi da yayi a ranar Alhamis, 8 ga watan Agusta, gwamnan ya ga laifin Oshiomhole akan rikicin da ya kunno kai a majalisar dokokin jihar.

Oshiomhole ya nemi a yi sabon shela akan rantsar da majalisar dokokin jihar Bauchi.

Amma da yake magana ta hannun kakakinsa, Ladan Salihu, gwamnan yace an magance rikicin da ke faruwa a majalisar dokokin jihar sannan kuma cewa lamarin ya zama tarihi.

“Mambobi majalisar takwas karkashin jagorancin Shugaban APC na kasa na daga cikin mutane 17 da aka rantsar a makon da ya gabata a zauren majalisar. Dukkanin yan majalisar 31 a yanzu sun kasance mambobin majalisar dokokin jiha guda,” Inji shi a cikin wata sanarwa.

Yayinda yake yaba ma alkawarin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na sanya baki a lamarin, Mohammed yace wadanda suka jagorancin kungiyar ne suka ragi Shugaban kasar da wasu bayanai saboda son ransu.

KU KARANTA KUMA: Tsananin talauci ne ya jefa ni harkar garkuwa da mutane - Mai laifi

“Gwamnati da mutanen jihar Bauchi, sun san cewa duk wani rikici a majalisar ya zama tarihi. A yanzu ya majalisar Bauchi sun zama tsintsiya madaurinki daya. Zance yin sabon sheda bai taso ba,” cewar jawabin.

“A bayyane yake cewa yan majalisarmu ba sune matsala ba, maimakon haka Oshiomhole na APC ne matsalar. Yana kokarin jefa zaman lafiyar siyasa cikin hatsari a jihar Bauchi. Wannan yayi bayanin dalilin da yasa ya tsame mambobin majalisar dokokin jihar Edo daga ziyarar fadar Shugaban kasa.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel