Babu ruwana da shafuka da ke dangantani da goyon bayan masu yi wa Buhari bore – Namadi Sambo

Babu ruwana da shafuka da ke dangantani da goyon bayan masu yi wa Buhari bore – Namadi Sambo

Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ya nesanta kanshi daga shafukan da ke yada wasu labaran karya kan cewa wai yana goyon bayan masu shirya yi wa gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari bore.

Jaridar Premium Tims ta ruwaito cewa Namadi yace ko kadan bashi bane ke da mallakin wadannan shafuka da ke watsa irin wadannan kalamai na batanci akan gwamnatin Buhari.

Namadi ya kara da cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an kama masu yada irin wadannan rade-radin da sunan sa domin a hukunta su.

“Ban taba yin amfani da shafukan sada zumunta na zamani ba ballantana in wallafa wani bayani ba, saboda haka duk wani bayani mai dauke da sunana a shafukan sada zumunta na FACEBOOK karya ce kuma ba daga gareni bane.

“Zanyi amfani da wannan damar in jawo hankalin jama’a cewa duk bayanan da ake wallafawa a shafukan sada zumunta na FACEBOOK da sauransu bani bane, hasalima sunayin haka ne domin haifar da rudani da kuma kawo rashin kwanciyar hankali.

KU KARANTA KUMA: An gurfanar da wani dan shekara 25 bisa laifin yi wa mahaifiyarsa mugun duka

“Marasa kishi da nuna son rai suke yunkurin bata min dangantaka na domin cimma bukatarsu na son rai” Inji Namadi Sambo.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, ya bayyana cewa baya shiga shafukan sada zumunta, akan haka, ya bukaci daukacin al’ummar kasar nan da su kauracewa karanta duk wani bayani wanda aka sanya sunanshi a shafukan sada zumunta na zamani suna isar da wasu sakonni na son rai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel