Eid-el-Kabir: Hukumar FRSC ta gargadi masu mota akan tukin ganganci

Eid-el-Kabir: Hukumar FRSC ta gargadi masu mota akan tukin ganganci

Hukumar da ke hana afkuwar hadarurruka (FRSC) ta gargadi masu tukin mota da su guje ma tukin ganganci da tsananin gudu gabannin bikin babban Sallah.

Legit.ng ta rahoto cewa kwamandan hukumar na jihar, Cecilia Alao, wacce ta bayar da gargadin a hiran da tayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Alhamis, 8 ga watan Agusta, ta bukaci masu mota da su bi ka’idoji a lokacin sallah da bayan sallah.

Tace mafi akasarin jami’an FRSC ba za su yi bikin babban sallah ba domin a tura su wurare daban-daban domin tabattar da tsare masu amfani da hanyoyi.

“Aikinmu ne tabbatar da tsaron al’umma da za su bi hanyoyi da kuma tabbatar da ganin mun yi aiki yadda ya kamata. Mun gudanar da taron wayarwa jama’a kai akan ilimin tuki gabannin bikin babban sallah.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kwamishinan zabe ya yi murabus domin shiga takarar gwamna a wata jihar kudu

“Abune da zai iya yiwuwa yin biki ba tare da hatsari ba idan har masu tuki za su iya bin ka’idar tuki. Sannan ya zama dole su guje ma gudun da ya zarce kima da kuma tukin ganganci,” inji Alao.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel