Karshen duniya: An kama wani da ya yi wa tsohuwa 'yar shekara 89 fyade

Karshen duniya: An kama wani da ya yi wa tsohuwa 'yar shekara 89 fyade

Asirin wani mutum dan shekaru 71 mai suna Yap Chaiphak ta tonu bayan an kama shi yana yi wa wata makwabciyarsa fyade a Kudancin Thailand.

Chaiphak ya amsa laifinsa bayan an mika shi hannun 'yan sanda.

Sai dai kafin ya shiga hannun 'yan sandan, wasu fusatattun matasa sun dandana masa kudarsa bisa mummunan abin da ya aikata.

Jikar tsohuwar da aka yi wa fyade mai suna Naphawan ta bayyana cewa ta doke Chaiphak sai hudu zuwa biyar da sandan tsintsiyar shara saboda rashin nadamar aikata abinda ya yi.

DUBA WANNAN: Zamfara: Tsohon mataimakin gwamna, Shugaban Majalisa da wasu da dama duk sun dunguma sun koma PDP

"Na fusata sosai," a cewar ta.

"Yanzu garin ba tsare gaskiya idan har makwabci zai iya yi wa makwabciyarsa irin wannan mummunan abin."

Wacce aka yi wa fyaden, mai suna Mia tana kwance ne a wani dankali a gaban gidanta da ke kauyen Ban Na a ranar Litinin.

Tuni dai an kwantar da wanda ake zargin a asibiti domin yi masa magani saboda hannunsa da ya karye da kuma rauni da ya samu a kirjinsa yayin da mutane suke nada masa na jaki.

A halin yanzu jami'an tsaron ba su bayyana ko za a gurfanar da mutumin a gaban kotu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel