Harin 'Yan bindiga: Shugaban karamar hukuma ya tsallake rijiya da baya a Taraba

Harin 'Yan bindiga: Shugaban karamar hukuma ya tsallake rijiya da baya a Taraba

Shugaban karamar hukumar Takum na jihar Taraba, Shiban Tikiari ya tsallake rijiya da baya a ranar Laraba yayin da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka bude wuta a motarsa yayin da ya ke kan hayarsa na zuwa kauyen su.

Tikiari ya shaidawa Channels TV cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a babban titin Takum zuwa Wukari a kauyen Kofa Ahmadu.

Ya bayyana cewa 'Yan sandan biyu da ke masa rakiya sun jikatta sakamakon harbin bindiga da maharan su kayi musu.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Gwamna Matawalle ya nada sabbin sakatarorin kananan hukumomi 14 a Zamfara

Shugaban karamar hukumar ya yi ikirarin cewa 'yan bindiga na kabilar Tibi ne suka kai masa hari a hanyarsa ta komawa Takum daga Wukari inda shi da takwarorinsa daga yankin kudancin jihar suka tafi ta'aziya a garin Donga da sarkinsu, Stephen Bayonga ya rasu a baya bayan nan.

"Munyi shirin haduwa ne a Rafinkada sannan sai mu tafi Donga don zuwa yiwa takwaran mu ta'aziyar rasuwar sarkin yankin. Amma da na isa can sai ban ga sauran takwarori na ba.

"Da na kira su a waya sai suka ce in same su a Wukari," a cewar sa.

A martaninsa, Shugaban Kungiyar 'Yan Tibi na jihar Taraba, Goodman Dahida ya ce bai san da labarin harin ba.

Sai dai mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, David Misal ya tabbatar da afkuwar harin da ya ce wasu da ake zargin 'yan daba ne suka kai kuma 'yan sanda biyu sun jikatta.

A cewarsa, Rundunar 'Yan sanda reshen Jihar Taraba tana aiki tukuru domin magance hare-haren 'yan daba a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel