Tsananin talauci ne ya jefa ni harkar garkuwa da mutane - Mai laifi

Tsananin talauci ne ya jefa ni harkar garkuwa da mutane - Mai laifi

Wani dalibin kwalejin ilimi na Obudu a jihar Cross River, Terfa Godwin, ya tona cewa yana da hannu a cikin harkar garkuwa da mutane sakamakon tsananin talaucin da yake ciki.

Kwamishinan yan sandan jihar Benue, Mukaddas Garba ne ya gurfanar da Godwin a ranar Alhamis, 8 ga watan Agusta tare da wasu masu laifin 14, a hedkwatar rundunar da ke Makurdi akan aikata laifuka daban-daban da suka ha da fashi da makami, kera makamai ba isa ka'ida ba da dai sauransu.

Yayin da yake magana da manema labarai, mai laifin wanda ya kasance dalibi a bangaren kimiyar siyasa/lissafi a kwalejin ilimin na Obudu, yace yayi nadama akan abunda ya aikata.

Godwin yayi ikirarin cewa ya kan rubuta wasika zuwa ga wadanda yake hari, inda yake razana su kan su biyan kudin fansa ko kuma a sace su bayan wadin da ke kunshe a wasikar.

Ya karbi bakin cewa yayi nasara wajen karban kudi daga hannun mutane uku ta hakan, inda ya kara da cewa ya kan daukaka harin ne shi kadai.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kwamishinan zabe ya yi murabus domin shiga takarar gwamna a wata jihar kudu

Biyu daga cikin wadanda ya kai ma hari masu suna Pande Emmanuel da Emmanuel Nenge sun kasance a hedikwatar, sannan kuma sun tabbatar da yanda mai laifin ke aiwatar da aikinsa, inda suka bayyana cewa ya rubuto ma kowannensu wasika, sannan ya kuma bukaci da su ajiye mishi kudi a kebabben wuri da kuma lokacin ajiyewa ko kuma ya sace matansa da yara.

A halin da ake cki, kwamishinan yan sandan yace dubun Godwin ya cika ne a lokacin da wani mutum daga karamar hukumar Vandekiya inda yafi aiwatar da ta'asarsa, ya kai rahoto ga yan sanda cewa wasu mutane da bai sani ba suna kiransa sannan suna masa barazana kan ya biya naira miliyan biyu ko kuma su yi garkuwa da shi sannan su kashe shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel