An gurfanar da wani dan shekara 25 bisa laifin yi wa mahaifiyarsa mugun duka

An gurfanar da wani dan shekara 25 bisa laifin yi wa mahaifiyarsa mugun duka

An gurfanar da wani matashi dan shekara 23, Sunday John a gaban wata kotun majistare da ke garin Ondo, jihar Ondo kan laifin yiwa mahaifiyarsa, Misis Virginia John dukan tsiya da sanda, inda ya ji mata rauni a duk ilahirin jikinta.

John wanda yan sanda suka gurfanar kan yiwa mahaifiyarsa duka da har sai da ta rasa inda kanta yake, ya yarda cewar ya aikata laifin.

Yan sandan sun kuma yi zargin cewa John yayi barazanar ji wani mai suna Ismaila Adedeji rauni, tare da muggan makamai lamar wuka, yayinda ya kuma yi abunda zai iya haifar da rikici ta hanyar rike mugun makami wajen fada a bainar jama’a.

A yanzu mai laifin na fuskantar tuhume-tuhume uku da suka hada da cin zarafi, barazana ga rayuwa da kuma kokarin haddasa tashin hankali.

Wanda ake karan ya aikata laifin ne a ranar 1 ga watan Agusta, 2019, da misalin karfe 8:00 na safe a gida mai lamba 6, unguwar Bolorunduro, Surulere a garin Ondo, karamar hukumar Ondo ta yamma da ke jihar Ondo.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kwamishinan zabe ya yi murabus domin shiga takarar gwamna a wata jihar kudu

Wanda ake karar wanda bai da lauya mai kare shi ya amsa laifi guda yayinda ya ki amsa sauran tuhume-tuhumen da ake masa.

Dan sanda mai kara, Mista Abiodun Adebiyi, ya sanya rana domin bashi damar yin nazari akan lamarin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel