Kisan 'yan sanda 3: Rundunar 'yan sanda ta yi wa rundunar sojin Najeriya tambayoyi 2 masu wuyar amsa

Kisan 'yan sanda 3: Rundunar 'yan sanda ta yi wa rundunar sojin Najeriya tambayoyi 2 masu wuyar amsa

A ranar Laraba ne rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da kisan jami'an ta uku da kuma raunata wasu da dama yayin da wasu dakarun sojojin Najeriya suka bude wa tawagar 'yan sanda wuta a jihar Taraba.

A cewar rundunar 'Yan sanda, lamarin ya faru ne a kan titin Ibi zuwa Jalingo.

Felix Adojie, mataimakin sufritandan 'yan sanda ya jagoranci tawagar 'yan sandan ne domin kamo wani mutum da ake zargin shugaban masu garkuwa da mutane ne da aka ce sunan sa, Alhaji Hamisu.

Sai dai, da yammacin ranar Alhamis, rundunar 'yan sanda ta aike da sakon wasu tambayoyi guda biyu ga rundunar sojin Najeriya dangane da kisan jami'anta guda uku da kuma sakin mai laifin da suka kama.

A cikin wasu gajerun sakonni da ta saki a shafinta na Tuwita, rundunar 'yan sanda ta ce, "idan har rundunar soji na ikirarin cewa sun kubutar da Alhaji Hamisu Bala Wadume ne bisa tunanin cewa an yi garkuwa da shi, me yasa basu dauke shi zuwa wata bariki ko ofishin rundunar soji ba domin daukar bayanansa da kuma gudanar da sauran matakan tsaro da rundunar soji ke dauka duk lokacin da ta kubutar da wani mutum ko mutane ba?

DUBA WANNAN: Malamin addini ya yi 'batan dabo' bayan ya dirka wa wata matashiyar marainiya ciki

"Me yasa suka harbi jami'an 'yan sanda duk da sun sanar da su tare da nuna musu shaidar cewar su ma'aikata ne kamar yadda kowa zai iya gani a cikin faifan bidiyon kisan 'yan sandan da yanzu haka ke yawo a kafafen yada labarai da dandalin sada zumunta?"

An ruwaito cewa dakarun sojin sun kashe sufetan 'yan sanda daya da wasu masu mukamin saja biyu tare da raunatta wasu. Sun kuma kashe farar hula guda daya.

Sai dai, a nata bangaren, rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun yi musayar wuta da wasu da suke tsamanin masu garkuwa da mutane ne da suka sace wani mutum a titin Ibi zuwa Wukari a jihar Taraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel