Zamfara: Tsohon mataimakin gwamna, Shugaban Majalisa da wasu da dama duk sun dunguma sun koma PDP

Zamfara: Tsohon mataimakin gwamna, Shugaban Majalisa da wasu da dama duk sun dunguma sun koma PDP

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Mukhtar Ahmad Anka da tsohon Kakakin Majalisar Jihar, Alhaji Bature Umar Sambo da tsohon sakataren gwamnatin jihar Alhaji Muhammad Bawa Gusau a ranar Alhamis run sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Sauran 'yan siyasan da suka koma jam'iyyar ta PDP sun hada tsohon kwamishinan matasa da koyar da sana'a, Alhaji Abdullahi Muhammad Burbin Baure da kansiloli 7 da ciyamomin mazabu 194 a jihar.

A yayin da ya ke jawabi yayin bikin karbar su a jam'iyyar, tsohon mataimakin gwamnan jihar Alhaji Mukhtar Ahmad Anka ya ce sun sauya koma jam'iyyar ta PDP ne saboda irin jagoranci na gari na Gwamna Bello Muhammad Mutawalle.

DUBA WANNAN: An fitar da sunaye da hotunan 'Yan sanda 3 da sojoji suka bindige a Taraba

Tsohon Kakakin Majalisar Jihar wanda ya ce ya koma jam'iyyar da magoya bayansa ne domin su tallafawa gwamnatin jihar a yunkurin ta na samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Tsohon Kwamishinan Matasa na jihar ya ce ya koma jam'iyyar ne tare da dimbin magoya bayansa.

A bangarensa, Gwamna Bello Mutawalle ya ce kofar gwamnatinsa a bude ta ke domin maraba da kowa kuma a shirye ya ke ya karbi shawara ko gyara da su kawo cigaban jihar.

"Muna kokarin samar da zaman lafiya a jihar mu kuma mun fara ganin sakamako. Wadanda ke zama a kauyuka za su tabbatar da hakan. Kasuwanci ya fara bunkasa saboda an fara bude kasuwannin kauye," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel