Kisan ‘Yan sanda: Sojoji da ‘yan sanda sun kafa kwamitin bincike na hadin gwiwa

Kisan ‘Yan sanda: Sojoji da ‘yan sanda sun kafa kwamitin bincike na hadin gwiwa

-Rundunar soji da hukumar 'yan sanda sun kafa kwamitin binciken yadda aka hallaka yan sanda uku a jihar Taraba

-Kanal Sagir Musa wanda shi ne kakakin rundunar sojin Najeriya ne ya bada wannan sanarwa inda ya ce DIG Mike Ogbizi ne zai jagoranci kwamitin

-Kanal Sagir ya ce babu wata magana da zasu sake yi a hukumance har sai binciken ya kai karshe

Rundunar Sojin Najeriya da ‘yan sanda sun kafa kwamitin hadin gwiwa domin yin bincike a kan dakarun Bataliya ta 93 dake Takum a jihar Taraba wadanda suka yi sanadiyar mutuwar wasu jami’an yan sanda ranar Talata 6 ga watan Agusta.

Kanal Sagir Musa wanda shi ne mukaddashin kakakin rundunar Sojin Najeriya shi ne ya bada wannan labara kunshe cikin wani zance da ya fitar a ranar Laraba 7 ga watan Agusta. A cewarsa Mataimakin Sufeto Janar mai kula da sashen miyagun laifuka wato CID ne zai jagoranci kwamitin binciken.

KU KARANTA:Ba Fulani ke kisan mutane a Kudu maso gabas ba – Miyetti Allah

Musa ya kara da cewa, Mike Ogbizi shi zai kasance jagoran binciken inda tare da shi a cikin kwamitin akwai jami’an sojoji.

Kamar yadda kakakin ya fadi: “ Zamu zuba ido har sai mun ga sakamakon da wannan kwamiti zai fitar a matsayin rahoton hakikanin abinda ya faru. Kafin samu rahoto a hukumance babu wata magana da zamu sake furtawa dangane da wannan lamarin.”

Kakakin rundunar sojin ya cigaba da cewa, “ dakarun sojin na kokarin dakatar da wata mota ne wadda take a cike makil da masu garkuwa da mutane inda yawansu ya kai akalla mutum 10.

Al’amarin ya fara ne a kan hanyar Ibi zuwa Wukari a cikin jihar Taraba. Motar da masu garkuwar suka shigo dauke take da wannan lamba makale a jikinta LAGOS MUS 564 EU. Anyi kokarin sai dasu amma sun ki tsayawa saboda kokarin ceto shugabansu sukeyi wanda aka kama.

Nan take suka fara sakin wuta, inda haka ya sanya dole sai da dakarun sojin suka mayar da martanin harbin. A yayin hakan ne mutum hudu suka mutu inda uku cikinsu yan sanda ne.” A cewar Sagir.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel