Yanzu Yanzu: Kwamishinan zabe ya yi murabus domin shiga takarar gwamna a wata jihar kudu

Yanzu Yanzu: Kwamishinan zabe ya yi murabus domin shiga takarar gwamna a wata jihar kudu

Kwamishinan zabe na jihar Cross River, Dr. Frankland Briyai ya yi murabus daga matsayinsa domin shiga takarar gwamna da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba a jihar Bayelsa.

Dr. Briyai ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 8 ga watan Agusta, yayinda yake zantawa da manema labarai a hedkwatar hukumar zabe da ke Calabar, babbar birnin jihar Cross River.

Yace, “Mutane na sun kirani, mutane na sun yarda da kokarina da kwazona na iya jagoranci.

“Sun yi imani dani sannan kuma sun yarda cewa zan iya kai Bayelsa da mutanenta matakin ci gaba da kuma next level."

Yace mutanen jihar sun yarda cewar zai dawo da martaba da albarkattunta.

KU KARANTA KUMA: Zaben Kano: Ganduje da Abba gida-gida na gab da sanin makomarsu, kotu ta sanya lokacin yanke hukunci

A nashi bangaren, Shugaban jam’iyyar CNPP, Sunday Micheal ya bayyana cewa Briyai ya kasance babban kadara ga Najeriya, inda ya Kara da cewa ya isar da aikinsa a matsayin kwanishinan zaben Cross River ta hanyar cimma nasarori da dama.

A wani labarin kuma mun ji cewa Sanata Ifeanyi Ubah na jam’iyyar YPP ya fara kare nasarar da ya samu a zaben bana a gaban kotun da ke sauraron karar zaben jihar Anambra a 2019.

Ifeanyi Ubah ya yi takara ne da Sanata Andy Uba na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya da kuma Kaninsa watau Cif Chris Uba na babbar jam’iyyar PDP mai hamayya.

Sanata Ifeanyi Ubah ya gabatar da shaidu 8 a gaban kotu a Ranar 7 ga Watan Agusta, 2019. Shaidu hudu ne su ka bayyana a gaban kowace shari’a da a ke yi da Sanatan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel