APC ta dakatar da mataimakin gwamnan Kogi

APC ta dakatar da mataimakin gwamnan Kogi

Jam’iyyar All Progressives Congress wato APC a jihar Kogi ta dakatar da mataimakin gwamnan jihar Simon Achuba daga zama dan jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar APC a jihar Abdullahi Bello ne ya bada wannan sanarwar a wata hira da yayi da manema labarai ranar Alhamis a Lokoja babban birnin jihar.

A cewarsa an dakatar da mataimakin gwamnan ne bisa zarginsa da yiwa jam’iyyar APC zagon kasa tun kafin a gudanar da babban zaben 2019.

KU KARANTA: A sake ba Fashola ministan lantarki, wata kungiya ta roki Buhari

Har ila yau, jam’iyyar ta APC ta dauki matakin dakatar da Simon Achuba bisa abin kunyar da take ganin ya jawo mata a jihar Kogi.

Bello ya ce: “ Mun dade muna samun korafe-korafe da dama daga mazabar Iyano wadda take karkashin karamar hukumar Ibaji inda shi mataimakin gwamnan ya fito. Labarin da ya zo mana shi ne Simon ya hada kai ne da ‘yan wata jam’iyya yana ha’intarmu.

“ A dukkanin zabukan da aka gudanar jam’iyyun adawa ya yima aiki ba APC. A don haka bayan mun gama tattara bayanan korafi daga bangaren gundumarsa ta Iyano da sauran masu ruwa da tsaki cikin lamuran APC a jihar Kogi muke yanke hukuncin cewa dakatar da shi ne abu mafi dacewa a yanzu.” Bello ya nanata.

Bugu da kari, shugaban jam’iyyar ya sake cewa, Achuba zai cigaba da zama a matsayin wanda jam’iyyar APC ta dakatar har sai sun ga amsar da zai bada a kan wasikar da suke shirin aika masa dangane da dakatarwar tasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel