Zaben Kano: Ganduje da Abba gida-gida na gab da sanin makomarsu, kotu ta sanya lokacin yanke hukunci

Zaben Kano: Ganduje da Abba gida-gida na gab da sanin makomarsu, kotu ta sanya lokacin yanke hukunci

Kotun sauraron korafe-korafen zaben gwamnan jihar Kano karkashin jagorancin Justis Halima Shamaki ta bayyana cewa, za a yanke hukunci akan karar da jam’iyyar Peoples Democratic Party,(PDP) ta shigar inda take kalubalantar nasarar Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a watan Oktoba.

Ta yi magana ne bayan lauyan da ke wakiltan masu kara, Barista Adegboyega Awomolo (SAN) a fada ma kotu cewa sun kai karshen gabatar da shari’arsu.

Justis Shamaki tace kotun zaben ba za ta amince da jinkiri daga wadanda ake kara ba.

Ta umurci INEC, Ganduje da APC su gabatar da hujjojin kare kansu a jere, inda yayi bayanin cewa da zaran kotu ta bude fagen sauraron wadanda ake kara, ba za ta amince da bukatar dage shari’ar ba.

A cewarta, “Idan daya daga cikin wadanda ake kara ya gama yau, mutum na biyu ya shirya washegari.”

Ta bayyana cewa suna aiki ne da lokaci domin haka ba za su lamunci kowani jinkiri ba.

KU KARANTA KUMA: Toh fah: Jerin jihohi 15 da za su fuskanci matsananciyar ambaliyar ruwa

Jam'iyyar Peoples Democratic Party, reshen jihar Kano ta maka INEC, Ganduje da kuma APC gaban kotun zabe isa zargin cewa ba gaskiya bane ikirarin cewa Ganduje ne ya ci zaben jihar da aka gudanar a ranar 23 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel