Sanata Ifeanyi Ubah ya soma kare kansa a kotu a game da zaben 2019

Sanata Ifeanyi Ubah ya soma kare kansa a kotu a game da zaben 2019

Mun samu labari cewa Sanata Ifeanyi Ubah na jam’iyyar YPP ya fara kare nasarar da ya samu a zaben bana a gaban kotun da ke sauraron karar zaben jihar Anambra a 2019.

Ifeanyi Ubah ya yi takara ne da Sanata Andy Uba na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya da kuma Kaninsa watau Cif Chris Uba na babbar jam’iyyar PDP mai hamayya.

Sanata Ifeanyi Ubah ya gabatar da shaidu 8 a gaban kotu a Ranar 7 ga Watan Agusta, 2019. Shaidu hudu ne su ka bayyana a gaban kowace shari’a da a ke yi da Sanatan.

Kowane daga cikin ‘Ya ‘yan gidan Uba su na kalubalantar nasarar da Sanata Ifeanyi Ubah ya samu a karkashin jam’iyyar YPP a zaben yankin Sanatan Anambra na Kudu.

Barista Chuma Ogunjiofor shi ne ya tsayawa Sanata Andy Uba na APC a karar, shi kuma babban Lauya George Igbokwe shi ne wanda ya ke kare Chris Uba a gaban kotu.

A duka shari’ar da a ke yi, babban Lauya Dee Nwigwe, shi ne wanda ya ke kare sabon Sanatan na YPP. Lauyan ya na ikirarin cewa YPP ce ta lashe wannan zaben da a ka yi.

KU KARANTA: Buhari ya fadawa manyan APC cewa zai ba su mukamai wannan karo

Daya daga cikin shaidun da su ka tsayawa Sanatan a kotu, ya bada shaidar cewa YPP ce ta lashe zaben ‘dan majalisar dattawa na yankin Kudancin Anambra a zaben Fubrairun.

Mista Chukwuma Uba, wanda ya yi aiki a matsayin Wakilin jam’iyyar YPP a zaben 2019, ya fadawa kotu cewa sun lashe zabe ne hankali kwance ba tare da wani magudi ba.

Wakilin na YPP ya tabbatar da banbancin kuri’un da a ka samu a zaben inda ya zargi hukumar zabe na kasa watau INEC da wannan kuskure a karamar hukumar Nnewi.

Sai dai mai gabatar da shaidar ya bayyana cewa ‘dan takararsa bai amfana da tsirarrun kuri’un da a ka soke ba, ya kuma bayyanawa kotu ya na fama da larurar ciwon idanu.

A cewarsa, wannan matsala ta ciwon ido ce ta hana shi ganin sakamakon zaben da kyau, ko da a ka bi shi aron tabarau, sai ya nuna cewa wannan tabarau ba na irin ciwonsa ba ne.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel