Ba Fulani ke kisan mutane a Kudu maso gabas ba – Miyetti Allah

Ba Fulani ke kisan mutane a Kudu maso gabas ba – Miyetti Allah

-Kungiyar Miyetti Allah ta nisan 'yan kungiyarta daga zargin da ake masu na cewa su ke aikata kashe-kashe a kudancin Najeriya

-Shugaban kungiyar reshen Kudu maso gabas Siddiki Gidado ne ya fitar da wannan bayani a hirarsa da manema labarai

-Akwai kabilu da dama wadanda ke aikata kashe-kashen amma a koda yaushe sai a ce ai Fulani ne a cewar Gidado

Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah reshen Kudu maso gabas ta Najeriya ta yi ikirarin cewa mafi yawan kashe-kashen da ake yi a yankin na Kudu maso gabas ba Fulani bane ke yinsa, wasu ‘yan bindiga ne da basu da wata alaka da Fulani.

Shugaban kungiyar reshen Kudu maso gabas, Alhaji Siddiki Gidado ya ce, duk da yake za a iya samun bata gari cikin kungiyarsu, sai dai ya kara da cewa akasarin kashe-kashen ba mutanensu ba ne ke aikatawa.

KU KARANTA:APC ta dakatar da mataimakin gwamnan Kogi

Shugaban ya fadi hakan ne a wata hira da yayi da jaridar The Guardian inda ya ce, mafi yawancin kashe-kashen wasu ne makiyaya na daban ke aikatawa amma ba Fulani makiyaya ba.

A cewarsa, makiyaya daga kabilun Igbo, Tiv, Bare-bari da Shuwa Arab su ne aikata wannan ta’asa.

“ A cikin ko wace kabila akwai bara gurbi, idan aka samu bangare guda ya aikata laifi sai tuhumi dukkanin al’ummar wannan kabilar. Ana yawan daurawa Fulani alhakin laifin da basu aikata ba.” Inji Gidado.

A wani labarin kuwa zaku ji cewa, wata kuniyar masu kananan sana’o’i ta mika kokon baranta zuwa ga Shugaba Buhari na cewa ya sake nada Fashola a matsayin ministan lantarki.

Kungiyar wadda ake yiwa inkiya da NASME reshen jihar Legas ta fitar da wannan sanarwar ne ta hannu shugabanta Solomon Aderoju inda ya ce, Fashola shi ne mafi dacewa da ma’aikatar lantarki saboda yayi kuma kowa ya yaba da aikinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel