Gbajabiamila ya saka wa 'yan majalisa 15 da suka janye masa takara da shugabancin kwamiti masu maiko

Gbajabiamila ya saka wa 'yan majalisa 15 da suka janye masa takara da shugabancin kwamiti masu maiko

Yawancin wadanda suka yi takarar neman shugabancin majalisar wakilai tare da shugaban majalisar na yanzu, Femi Gbajabiamila, sun samu mukami a zauren majalisar, wasu kuma sun samu shugabancin kwmiti masu maiko.

Wasu kuma an basu jagorancin wasu kwamiti na musamman.

A kalla mambobin majalisar wakilai 20 e suka nuna sha'awarsu ta yin takarar kujerar shugaban majalisa, kuma mafi yawansu daga baya sun janye wa shugaban masu rinjaye a zauren majalisar, Femi Gbajabiamila, wanda yanzu shine kakakin majalisar.

Goma sha biyar daga cikin wadanda suka yi nuna sha'awar yin takarar kujerar shugaban majalisar wakilai sun samu mukami a karkashin shugabancin Gbajabiamila.

Idris Wase ya zama mataimakin shugaban majalisar wakilai, yayin da Alhassan Ado Doguwa ya zama shugaban masu rinjaye.

Mohammed Monguno (mamba a APC daga jihar Borno) ya zama bulaliyar majalisa, yayin da Nkeiruka Onyejeocha (mamba a APC daga jihar Abia) ta zama mataimakiyar bulaliyar majalisa.

Wadanda suka samu shugabancin kwamiti masu maiko sun hada da; Mohammed Bago, wanda shine mutum daya tilo da bai janye wa Gbajabiamila takararsa ba.

DUBA WANNAN: Wata budurwa ta rataye kan ta saboda ta yi cikin shege

Yanzu shine shugaban kwamitin hadin kai da mu'amala a tsakanin kasashen Afrika.

John Dyegh, wanda ya janye wa Gbajabiamila takara an gobe zabe, ya samu zama shugaban kwamitin majalisa a kan hakkin bil'adama.

Ragowar mambobin majalisar da suka samu mukamin shugabantar kwamiti sun hada da; Muktar Betara (Borno), kwamitin kasafi; Khadijat Bukar-Ibrahim (Yobe), kwamitin cigaban yankin arewa maso gaba; Abdulrazak Namdas (Adamawa), kwamitin kula da harkokin sojoji; Aminu Suleiman (Kano), kwamitin manyan makarantu; Babangida Ibrahim (Kano), kwamitin kula da saka hannun jari da cibibiyoyin hada-hadar kudi; Olusegun Odebunmi (Oyo), kwamitin yada labarai da wayar da kan jama'a da tabbatar da da'a, da Gudaji Kazaure (Jigawa), kwamitin kula da jam'iyyun siyasa.

Sauran sune; Yakub Buba (Adamawa), kwamitin kula da harkokin da suka shafi kasashen ketare; Abubakar Lado (Niger), kwamitin labarai da kimiyyar sadarwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel