Buhari ya ja labule da Gwamnan Adamawa a Villa

Buhari ya ja labule da Gwamnan Adamawa a Villa

Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga wata ganawar sirri da Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri tare da tawagarsa.

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri shi ne ya jagoranci tawagar tasa zuwa Fadar Shugaban kasa ta Villa dake Abuja.

KU KARANTA:A sake ba Fashola ministan lantarki, wata kungiya ta roki Buhari

An shiga wannan ganawar ne da misalin karfe 2:58 na ranar Alhamis 8 ga watan Agusta, 2019 a cikin dakin taro na Fadar Shugaban kasan.

Haka zalika, akwai sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha a cikin ganawar wanda ya fito daga jihar ta Adamawa da kuma shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Abba Kyari.

Ana cigaba da wannan tattaunawa a lokacin kawo maku wannan rahoton.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel