Babbar Sallah: Tambuwal ya ware wa marayu miliyoyin naira don yi musu hidima

Babbar Sallah: Tambuwal ya ware wa marayu miliyoyin naira don yi musu hidima

Gwamnatin Jihar Sokoto, a ranar Alhamis ta rabawa Hakimai 86 zunzurutun kudi Naira miliyan 17.2 domin sayan shanu da za a yankawa marayu a jihar yayin bikin Eid el-Kabir wato Sallah babba.

Shirin da aka saba yi duk shekara an hannun Cibiyar Zakka da Tallafawa Al'umma da aka kaddamar a fadar Sarkin Musulmi da ke Sokoto.

A yayin kaddamar da shirin rabon kudin, Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III ya gargadi Hakiman da kada su karkatar da kudaden ko jefa siyasa cikin lamarin.

DUBA WANNAN: Cin amana: Nayi nadamar kyalle mata ta shiga siyasa - Wani magidanci ya fada wa kotu

"Wannan shirin na gwamnatin ne domin tallafawa marayu, ba ta da alaka da wani mutum ko wasu 'yan wata jam'iyyar siyasa.

"Saboda haka, ya kamata mu kasance masu adalci ga gaskiya a garuruwan mu domin mabiyan mu su girmama mu."

Sarkin musulmim ya yabawa hakiman bisa kokarin da su kayi wurin rabon kayan sallar a bara, ya kuma bukaci su cigaba da irin jajircewar a wannan shekarar kuma su kara tsoron Allah.

Sarkin ya mika godiyarsa ga gwamnatin jihar da hukumar Zakka saboda cigaba da shirin.

Ya yi addu'ar Allah ya karbi ibadun dukkan al'ummar musulmi kuma ya bukaci su rika yi wa kasa addu'ar samun zaman lafiya.

A baya, Shugaban Kwamitin na Zakka, Malam Muhammad Maidoki ya ce shirin na cikin tsare-tsaren gwamnatin jihar ne don tallafawa marayu da marasa karfi a gari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel