Kotu ta hana majalisar dokokin tarayya karbe ragamar majalisar dokokin Edo

Kotu ta hana majalisar dokokin tarayya karbe ragamar majalisar dokokin Edo

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta hana majilisun dokokin tarayya guda biyu kare ragamar majalisar dokokin jihar Edo.

Alkalin da ke sauraron karar, Taiwo Taiwo, a wani dan takaitaccen hukunci, ya umurci bangarorin da lamarin ya shafa da su bar komai a yadda yake, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci akan karar da kakakin majalisar dokokin Edo, Mista Francis Okiye ya shigar.

Justis Taiwo y adage sauraron shari’ar har zuwa ranar 22 ga watan Agusta, sannan ya umurci majalisar dokokin tarayya da ta amsa karar da ke kalubalantar shirin yan majalisun tarayya na karbe ragamar majalisar dokokin jihar Edo cikin makonni biyu.

Hakan na zuwa ne a daidai lokcin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ayar da tabbacin cewa zai yi aiki tare da hukumomin tsarin mulki daban-daban domin magance rkice-rikicen majalisun dokokin jihohin Bauchi da Edo.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock

Shugaban kasar ya kuma bukaci yan majalisar dokokin jihar da kad su bayar yancinsu da yancin wadanda suka zabe su, inda ya nemi da kada su raba kan majalisar da jam’iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel