A sake ba Fashola ministan lantarki, wata kungiya ta roki Buhari

A sake ba Fashola ministan lantarki, wata kungiya ta roki Buhari

-Kungiyar NASME reshen jihar Legas ta roki Shugaba Muhammadu Buhari ya sake ba Fashola rikon ma'aikatar wutar lantarki ta kasa

-Shugaban kungiyar masu kananan sana'o'i reshen jihar Legas Solomon Aderoju ne ya mika wannan kokon baran a madadin 'yan kungiyarsa

-Aderoju ya bayyana irin cigaban da Fashola ya kawo a fannin lantarki duk da cewa a wancan lokacin yana rike ne da ma'aikatu har uku

Kungiyar masu kananan sana’o’i ta kasa wato NASME reshen Jihar Legas sun roki Shugaba Muhammadu Buhari kan ya sake nada Fashola a matsayin ministan lantarki na kasa, inda suke cewa babu abinda ya samu lantarkin idan ba nakasu bayan barinsa wurin.

Da yake magana a madadin kungiyar NASME reshen jihar Legas, shugaban kungiyar Solomon Aderoju ya yabawa zababben ministan bisa namijin kokarin da yayi na kawo gyara a bangaren wutar lantarki, duk da cewa an hada masa ma’aikatu manya guda uku a wancan lokacin.

KU KARANTA:Gwamnoni sun dau alkawarin tsamo ‘yan Najeriya miliyan 50 daga talauci

Aderoju wanda ya bayyana muhimmancin da wutar lantarki ta ke da shi wurin bunkasa tattalin arziki ya ce akwai bukatar sake bada kulawa ta musamman a bangaren wutar. Inda ya ce ya tabbatar Fashola zai iya yin wannan aikin.

“ Dukkaninmu mun san muhimmancin lantarki wurin kawo cigaba ayyukan raya kasa da kuma tattalin arziki, muna da bukatar jajirtaccen mutum kamar Fashola a ma’aikatar lantarkin Najeriya.

“ Ko shakka babu mun ga irin cigaban da ya kawo mana a lokacin day a kwashe yana rike da ma’aikatar. Ba a nan ya kamata a tsaya ba akwai bukatar cigaba da wannan namijin aiki har sai an wadatar bukatun ‘yan Najeriya a fagen lantarki musammman masu kananan sana’o’i.

“ Ba lallai sai an sake ba shi duka ma’aikatun uku ba, ko da ma’aikatar lantarkin kadai aka ba shi muna da yakinin cewa zai ba mara da kunya domin zai share mana kukanmu.” Inji Aderoju.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel