Kotu ta daure wasu abokai 2 da suka sace doya guda 700

Kotu ta daure wasu abokai 2 da suka sace doya guda 700

Rundunar Yansandan jahar Benuwe ta gurfanar da wau abokai biyu gaban wata kotun majistri dake zamanta a garin Makurdi a kan zarginsu da satar doya kwara dai dai har guda 700, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yansanda na tuhumar abokai biyu da suka hada da Emberga Tyokyaa da Boniface Yahemba, da tuhume tuhume guda hudu da suka hada da hadin baki, kutse, cuta da sata.

KU KARANTA: EFCC za ta tasa keyar tsohon shugaban INEC gaban kotu kan satar naira biliyan 1.2

Dansanda mai shigar da kara, Sajan Godwin Ato ya shaoda ma kotu cewa wani manomi mazaunin karamar hukumar Gwer ta gabas, Tersee Adue ne ya kai karar abokan biyu da wasu mutane biyu da a yanzu haka sun tsere, cewa sun yi masa kutse a cikin gonarsa.

Tersee yace mutanen hudu sun tafka mummunan barna a gonarsa inda ya shuka doya na sama da naira dubu 70. Sai dai Dansandan yace har yanzu basu kammala gudanar da bincike a kan batun ba.

Amma Sajan Ato ya shaida ma kotu cewa laifukan da ake tuhumar mutanen biyu dashi ya saba ma sashi na 97, 349, 329 da 288 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Benuwe. Sai da mutanen biyu sun musanta aikata laifukan.

Don haka Alkalin kotun, Ajuma Igama ta bada belin abokan biyu a kan kudi N100,000 kowannensu, tare da mutane biyu da zasu tsaya musu a kan naira dubu dari dari, kuma ma’aikatan gwamnati daga mataki na GL07.

Daga karshe Alkali Igama ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Agusta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel