Babbar Sallah: Gwamna Babagana ya yi ma ma’aikatan jahar Borno sha tara na arziki

Babbar Sallah: Gwamna Babagana ya yi ma ma’aikatan jahar Borno sha tara na arziki

Gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zulum ya bada umarnin biyan kafatanin ma’aikatan gwamnatin jahar Borno albashinsu na watan Agusta domin su samu daman walawa a yayin bukukuwan babbar Sallah.

Jaridar Blue Print ta ruwaito gwamnan ya bada wannan umarni ne da yammacin Talata, 6 ga watan Agusta, ga shugaban ma’aikatan jahar Borno, Alhaji Mohammed Hassan, inda ya umarceshi ya biya ma’aikata albashinsu kafin ranar Juma’a, 9 ga wata.

KU KARANTA: An yi turereniya wajen kwasan wasu miliyoyin kudi da suka antayo daga cikin Motar banki

Haka zalika gwamnan ya umarci a biya wasu ma’aikata 9,898 alawus dinsu na hutu na shekarar 2018 wanda suke bin gwamnati bashi, sa’annan ya amince a biya hakkokin wasu yan fansho 185 da suka mutu ga iyalansu, da kuma wasu yan fansho 236 dake raye, kudin daya kai naira miliyan 773.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ko a watan data gabata, watan Yuli, sai da gwamnan ya biya wasu yan fansho su 1,684 hakkokinsu da suka yi ritaya tun a shekarar 2013. Bugu da kari gwamnan ya umarci ma’aikatan kudi ta tabbata ta biya wadannan kudade cikin kwanaki 3 kacal.

Gwamnan ya sake bada umarnin a biya wasu manyan sakatarorin ma’aikatun jahar Borno guda biyu daya tarar dasu a bakin a ranar daya kai ziyarar ba zata zuwa sakatariyar gwamnatin jahar, Musa Usman Secretariat a ranar 31 ga watan Mayun 2019, alawus din kayan daki.

A wani labarin kuma Gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki ya bada umarni ga babban akantan jahar Edo da kwamishinan kudi na jahar dasu gaggauta biyan ma’aikatan jahar albashinsu na watan Agusta domin Musulmai su gudanar da shagulgulan babbar Sallah cikin yalwa.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin zaman majalisar zartarwar jahar daya gudana a ranar Laraba, 7 ga watan Agusta a fadar gwamnatin jahar dake Bini, inda yace a biya duk ma’aikacin daya bukaci albashinsa na watan Agusta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel