Abdulmumin Jibrin ya yi hannunka mai sanda akan dakatarwar da APC tayi masa

Abdulmumin Jibrin ya yi hannunka mai sanda akan dakatarwar da APC tayi masa

- Honourable Abdulmumin Jibrin ya yi ba’a akan dakatarwar da APC tayi masa

- Dan majalisar tarrayar kasar a wani rubutu da ya wallafa a shafin sada zumunta ya yi hannunka mai sanda kan dakatarwar da jam’iyyar tayi masa

- Hakazalika ya bayyana cewa ya karbi bakuncin kansiloli da shugabanni wadanda suka kawo masa ziyarar ban girma

Abdulmumin Jibrin wanda ya kasance mamba a majalisar wakilai daga jihar Kano ya yi ba’a game da dakatar dashi da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tayi.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na twitter, dan majalisar yayi ba’a game da rashin kwamiti a majalisar cewa a yanzu shine Shugaban kwamitin majalisar akan rainon yara.

A yayinda yake Magana kan dakatarwar da APC tayi masa, dan majalisar yace ya karbi bakuncin zababbun kansilolin karamar hukumar Bebeji da kuma shugabannin APC na yankin da sakatarorin jam’iyyar da kuma jami’an karamar hukumar ciki harda masu ruwa na tsaki na karamar hukumar Bebeji da Kiru, inda suka kai masa ziyarar ban girma.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel