Da duminsa: Kotu ta bawa EFCC izinin tsare tsohon shugaban INEC

Da duminsa: Kotu ta bawa EFCC izinin tsare tsohon shugaban INEC

A ranar Alhamis ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta bawa hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) izinin cigaba da tsare tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta (INEC), Farfesa Maurice Iwu, har zuwa lokacin da kotun zata saurari bukatar neman belinsa da lauyan da ke kare shi ya mika wa kotun.

Kafin hukuncin kotun, EFCC ta gurfanar da Iwu a gaban mai shari'a Jastis Chuka Obiozor bisa tuhumarsa da aikata laifuka guda hudu da suka hada da boye wa da safarar kudin da yawansu ya kai biliyan N1.2.

A baya, Legit.ng ta sanar da ku cewa tsohon shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Maurice Iwu ya iso Kotun Tarayya da ke Legas domin gurfana gaban alkali.

Hukumar Yaki da Masu Yiwa Arzikin Kasa Ta'annati (EFCC) ce ta gurfanar da Iwu bisa tuhumar da ake masa na damfara ta naira biliyan 1.2.

DUBA WANNAN: NNPC ta bayyana dalilin karin kudin farashin Kalanzir

A cewar EFCC, ta gurfanar da Farfesa Iwu ne bisa tuhumarsa da aikata laifuka hudu masu alaka da karkatar da kudin gwamnati da kuma boye su.

EFCC ta yi ikirarin cewa tsakanin watan Disamban shekarar 2014 zuwa watan Maris din 2015, Iwu ya boye Naira biliyan 1.2 a asusun ajiyar kamfanin 'Bioresources Institute of Nigeria Limited' da ke bankin 'United Bank for Africa Plc' da aka fi sani da 'UBA'.

Hukumr EFCC ta yi zargin cewa kudin na daga cikin Naira Biliyan 23.29 da tsohuwar ministar albarkarun man fetur, Diezani Allison Madueke, ta raba domin tafka magudi a zaben shugaban kasa na shekarar 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel