Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, 8 ga watan Agusta, ya yi ganawar sirri tare da shugabannin tsaro.

Sun fara ganawar ne da misalin karfe 10:30 a safe a ofishin shugaban kasa da ke fadar Aso Rock.

An tattaro cewa tattaunawar nasu zai ta'allaka ne akan lamarin tsaro a kasar ciki harda fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma ta'aaddanci.

Har yanzu suna kan ganawar a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wata babbar Rundunar ‘Yan sandan Najeriya sun yi nasarar kashe wani rikakken ‘Dan fashi da makami kuma mai garkuwa da mutane wanda a ke kira Abacha.

Wannan hatsabibin mai laifi shi ne shugaban ‘yan fashin da su ka hana mutanen Yankin Emohua sakat a cikin jihar Ribas.

Abacha ya mutu ne a lokacin da ya ke fada da Dakarun ‘yan sandan kasar nan. A wajen wani gumurzu ne da a ka yi tsakanin wannan ‘dan fashi da ‘yan sandan Najeriya a ka harbe sa da bindiga har lahira. Wannan abu ya faru ne a sansanin Rumuakunde a cikin Garin Emohua.

Kamar yadda manyan jami’an ‘yan sandan jihar Ribas su ka bayyana, Dakarun tsaron sun kai wa manyan fashin hari ne inda su ka yi dace, su ka karbe wasu manyan makamai da Miyagun ke ta’adi da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel