Wasu sun shiga har dakin hukumar Kwastam sun saci kwayayoyi a Ribas

Wasu sun shiga har dakin hukumar Kwastam sun saci kwayayoyi a Ribas

Jami’an hukumar Kwastam na shiyyar Onne a jihar Ribas sun bayyana cewa sun damke wasu mutane biyar da su ka fasa wani akwati mai cike miyagun kwayoyi da su ka karbe kwanaki.

Babban jami’in hukumar masu yaki da fasa kauri na yankin, Aliyu Saidu ya bayyana cewa wadannan mutane sun dauke kwalin kwayoyi har sun jefa su a wasu motoci kafin a cafke su.

Kamar yadda mu ka samu labari a Ranar Alhamis, 8 ga Watan Agusta, 2019, jami’an Kwastam su ka kama wadannan mutane da su ka yi kokarin awon gaba da wasu dinbin kwayoyi na tramadol.

Daga cikin kwayoyin da a ka nemi su sace daga akwatin adanan Kwastam mai taku kafa 40 akwai; kwali 14 na wasu kwayoyi masu karfi da kwali 5 na wasu magungunan da ke sa barci.

KU KARANTA: Hukumar kwastam ta kama motar asibiti cike da kwayoyi

Haka zalika Said ya bayyana cewa wadannan mutane sun yi kokarin yin gaba da wasu kwali 2 na kwayoyin tramadol daga cikin wannan akwatin ajiya da su ka fasa kafin dubun su ta cika.

Bugu da kari wadannan mutane masu ta’adi sun yi kokarin biyan Ma’aikatan kwastam da ke kan aiki kudi har Naira miliyan 1 domin a bar su, su tsere. A karshe dai hakarsu ba ta cin ma ruwa ba.

Babban jami’i A. Saidu da ya ke magana a madadin daukacin hukumar da ke yaki da fasa kauri a Najeriya, ya bayyana cewa an nada wani kwamiti da zai binciki wannan lamari cikin gaggawa.

Haka zalika an karbe motoci biyu da a ka yi kokarin amfani da su wajen tserewa da wadannan kwayoyi, bayan nan an kuma garkame wadannan Barayi. Batun ya kai gaban kotu a halin yanzu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel