Hatsari: Mutane 20 sun kone kurmus a Bauchi

Hatsari: Mutane 20 sun kone kurmus a Bauchi

Kimanin rayukan mutane 20 ne suka salwanta a yayin wani mummunan hatsarin mota na daren ranar Juma'a da ya auku a kan hanyar Potiskum zuwa Sade dake karamar hukumar Misau ta jihar Bauchi.

Duk da cewar ba gano ainihin musabbabin aukuwar wannan hatsari ba, maruwaito rahoton sun bayyana cewa hatsarin ya auku yayin da wasu motocin haya biyu suka gwabza da junansu wanda hakan ya yi sanadiyar salwantar rayukan fasinjojin dake cikin su.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Bauchi, Kamal Abubakar, ya bayar da tabbacin aukuwar wannan mumman tsautsayi yayin ganawa da manema labarai na jaridar The Punch a wata hira da ta gudana tsakaninsu da Yammacin ranar Asabar ta hanyar wayar tarho.

DSP Kamalu ya ce hatsarin da ya auku tsakanin wasu motocin haya biyu kirar J5 dauke da awaki da kuma Hummer Bus wadda ta kama da wuta dauke da fasinjoji da misalin karfe 9.30 na daren ranar Juma'a, ya salwantar da rayukan mutane 20 nan take a yayin da suka kone kurmus.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Gbajabiamila ya gamu da Aisha Buhari a Makkah

Babban jami'in dan sandan ya ce na gudanar da jana'izar mamatan da misalin karfe 9.00 na safiyar ranar Asabar a garin Darazo na karamar hukumar Darazo a garin na Bauchin Yakubu.

A wani rahoton na daban da jaridar Legit.ng ta ruwaito, majalisar dinkin duniya ta gano cewa manoman tumatir a jihar Kano na tafka asarar kimanin kaso 40 cikin 100 na amfanin gona a duk shekara sanadiyar rashin ilimin fasahar zamani wajen sarrafawa da kuma tanadin amfani.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel