Rage cin nama zai taimaka wajen magance sauyin yanayi - UN

Rage cin nama zai taimaka wajen magance sauyin yanayi - UN

Majalisar dinkin Duniya reshen kula da sauyin yanayi, ta yi gargadin cewa rage cin nama da kuma mayar da cima gami da dogaro bisa kayan itatuwa, zai taimaka kwarai da gaske wajen magance barazanar sauyin yanayi a duniya.

Sabon binciken da majalisar ta fitar a baya-bayan nan ya tabbatar da cewa, yadda ake amfani da kasa wajen shuka tsirrai masu samar da abinci, zai taka rawar gani wajen magance matsaloli na dumamar yanayi da kuma samuwar wadataccen arziki na abinci a fadin duniya.

A rahoton da majalisar dinkin Duniya ta fitar a ranar Alhamis, ta ce watsi da wannan sabon bincike zai ci gaba da haifar da barazana ga kiwon lafiyar bil Adama masu alaka da sauyin yanayi.

Ta ce ci gaba da karuwar adadin al'umma a doron kasa gami da amfanin da mutane ke yi da kasa da ruwa a zamantakewa, ya na da babbar alaka ta haifar da sauyin yanayi.

Majalisar ta yi kira da a koma noma da shuka tsirrai masu samar da abinci da a cewarta mayar da su cima gami da rage dogaro a kan cin naman dabbobi, zai bayar da gagarumar gudunmuwa ta saukaka dumamar yanayi wato Global Warming a turance.

KARANTA KUMA: Gwamna Ihedioha ya fadi ma'aikatu da kwamishinonin jihar Imo za su jagoranta

Cikin binciken mai shafi 60 da majalisar dinkin Duniya ta gabatar yayin taron da ta gudanar a birnin Geneva na kasar Switzerland, ta ce dumamar yanayi na haifar da barazana ta kwararowar hamada, karancin ruwan sama, fari, asarar kasar noma gami da kuma konewar amfanin gona.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, tabbas idan aka rage dogaro wajen cin nama kuma aka koma dashen itatuwa da shukka tsirrai gami da kama harkokin noma gadan-gadan, barazanar dumamar yanayi za ta yi sauki a fadin duniya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel