Gwamna Ihedioha ya fadi ma'aikatu da kwamishinonin jihar Imo za su jagoranta

Gwamna Ihedioha ya fadi ma'aikatu da kwamishinonin jihar Imo za su jagoranta

A ranar Laraba cikin birnin Owerri, sabon gwamnan jihar Imo Emeka Ihedioha, ya rantsar da sabbin kwamishinonin gwamnatin sa 18 tare da gargadin su a kan tsayuwa bisa gaskiya yayin sauke nauyin da rataya a wuyansu.

Gwamna Ihedioha ya ce kasancewarsu hadimai a gare shi, ba ya nufin su cika umarninsa ba tare da manufa ta yiwa al'ummar jihar Imo bauta ba. Ya shawarci sabbin kwamishinonin a kan jin tsoron Mahallacinsu yayin kiransu da su yi aiki tukuru wajen ciyar da jihar Imo gaba.

Tsohuwar ministan harkokin kasashen ketare na Najeriya, Farfesa Viola Onwumere, na daya daga cikin sabbin kwamishinoni 18 da gwamna Ihedioha ya rataya wa nauyin al'umma.

Ga dai sunayen kwamishinonin da kuma ma'aikatu da za su jagoranta:

1. Ma'aikatar Shari'a – Ndukwe Nnawuchi

2. Ma'aikatar Kudi – Prof. Uche Uwaleke Ihitte Uboma

3. Ma'aikatar Kasuwanci da Masana'antu – Mr. John. Ekezie Okeahialam

4. Ma'aikatar Noma da Ma'adanai – Chief Emma Nworgu

5. Ma'aikatar Lafiya – Dr. Vin Udokwu

6. Ma'aikatar Kula da jin dadin al'umma – Hon. Chuma Nnaji

7. Ma'aikatar Ilimi – Prof. Mrs. Viola Adaku Onwuliri

8. Ma'aikatar Ayyuka – Engr. Benjamin Ekwueme

9. Ma'aikatar Tsare-Tsaren kasa – Sir. Bon Unachukwu

10. Ma'aikatar Matasa da ci gaban al'umma – Eronini Okechukwu Unaeze

11. Ma'aikatar Zamantakewa – Hon. Tony Okere

12. Ma'aikatar Yada Labarai da wayar da kai – Barr. Emeka Felix Ebiliekwe

13. Ma'aikatar Jinsi da harkokin kula da gajiyayyu – Chief Mrs. Nkeiru Ibekwe

14. Ma'aikatar Al'adu da yawan bude ido – Barr. Chijioke Nzekwe

KARANTA KUMA: Barazana: Tsohon gwamna Yari zai dauki mataki a kan wasu kafofin watsa labarai

15. Ma'aikatar Ci gaban kimiya – Mr. Meekam Mgbenwelu

16. Ma'aikatar Sufuri – Engr. Sly Enwerem

17. Ma'aikatar Kasafin Kudi da tattalin arziki – Mr. Reginald Ihebuzor

18. Ma'aikatar Gidaje – Mr Nicholas Anayo Amaefule

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel